Rundunar Sojin Najeriya A Jiya Ta Kammala Horas Da Dakaru 172 Domin Aikin Wanzar Da Zaman Lafiya A Kasar Guinea Bissau.

0 86

Rundunar sojin Najeriya a jiya ta kammala horas da dakaru 172 domin aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Guinea Bissau.

Sojojin sun fara atisayen tun a ranar 21 ga watan Maris a cibiyar kula da zaman lafiya ta Martin Luther Agwai da ke Jaji a jihar Kaduna.

Da yake jawabi ga sojojin, babban hafsan rundunar, Manjo Janar Taoreed Lagbaja, ya ce sojojin za su kasance bangare na dakarun zaman lafiya na Najeriya kashi na 2 a tawagar tallafawa ta kungiyar ECOWAS a kasar Guinea Bissau.

Taoreed Lagbaja, wanda ya samu wakilcin darakta mai kula da ayyukan tallafawa zaman lafiya, Manjo Janar Bayode Adetoro, ya ce bikin yaye daliban ya kara tabbatar da aniyar Najeriya na tura dakaru masu inganci a wani bangare na gudunmawar da take bayarwa wajen samar da zaman lafiya da tsaro a duniya.

Ya bayyana cewa horon da aka bayar kafin tura su an yi ne da nufin wayar da kai da ilimintar da sojoji akan aikin samar da zaman lafiya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: