An rantsar da sabbin masu yiwa kasa hidima fiye da 1800 da aka turo jihar Jigawa

0 54

An rantsar da sabbin masu yiwa kasa hidima maza da mata kusan dubu 1 da 800 na zango na uku rukuni na biyu na shekarar 2021 da aka turo jihar Jigawa domin yiwa kasa hidima.

A sakon da ya aike dashi wajen bikin da aka gudanar a sansanin horas da masu yiwa kasa hidima, babban daraktan hukumar na kasa Birgediya Janar Shuaibu Ibrahim ya taya masu yiwa kasa hidimar murnar kammala karatunsu da kuma samun damar zuwa aikin yiwa kasa hidima.

Babban daraktan wanda ya samu wakilcin shugabar hukumar ta jiha Hajiya Aisha Abubakar ya bukaci masu yiwa kasa hidimar da su tabbatar ana damawa dasu a dukkannin al’amurran da ake gudanarwa a sansanin horas da masu yiwa kasa hidimar.

Yace zasu sami horo a bangarori daban-daban da kuma na sanao’i’n dogaro da kai tare da fatan zasu yi kyakkyawar mu’amula da mutanen Jigawa domin morar aladu da dabi’unsu.

Aisha Abubakar ta kuma hore su dasu guji ta’amali da miyagun kwayoyi tare da kiyayewa da dokokin aiki na masu yiwa kasa hidima, da kuma kare dokokin kariya daga cutar corona.

Leave a Reply

%d bloggers like this: