An rufe kwalejin Adamawa biyo bayan zanga-zangar ɗalibai kan rashin wutar lantarki

0 566

Kwalejin fasaha ta jihar Adamawa da ke arewacin Najeriya ta rufe makarantar tsawon mako ɗaya sakamakon zanga-zangar da ɗalibai suka gudanar.

Bayanai sun ce zanga-zangar ta ɓarke ne sakamakon rashin ruwa da lantarki da ɗaliban makarantar ta Adamawa State Polytechnic, Yola suke fama da shi.

Hukumar makarantar ta ce ta rufe makaranta tsawon mako ɗaya tun daga yau Litinin.

“An ɗauki matakin ne domin bai wa hukumomi damar gyara lantarkin,” a cewar wata sanarwa da rajistran makarantar Simnawa Ayuba ya sanya wa hannu.

“An umarci ɗalibai su fice daga kwalejin kafin ƙarfe 12:00 na rana.”

Leave a Reply