An rufe wani masallaci a yankin arewacin kasar Faransa saboda hudubobin da wani limami ya yi

0 98

An rufe wani masallaci a yankin Oise da ke arewacin kasar Faransa saboda hudubobin da wani limami ya yi, wanda aka ce yana kare jihadi.

Hukumomin yankin sun ce masallacin da ke garin Beauvais zai kasance a rufe na tsawon watanni shida.

Hakimin Oise ya ce hudubobin da aka yi a masallachi sun bayyana mayakan jihadi a matsayin jarumai, tare da haddasa kiyayya da tashin hankali.

Hukumomi sun ba wa masallacin kwanaki 10 ya mayar da martani.

Limamin masallacin ya musulunta ne kwanannan.

Kasar Faransa na cigaba da gudanar da bincike kan masallatan da ake zargin suna da alaka da tsattsauran ra’ayi.

Makwanni biyu da suka gabata ne ministan cikin gidan kasar Gérald Darmanin ya ce ya fara shirin rufe babban masallacin Beauvais mai tazarar kilomita 100 daga arewacin birnin Paris, saboda zargin da ake yi wa limamin na cewa yana sukar kiristoci da masu neman maza da yahudawa a cikin hudubobinsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: