An samu hadurran tituna dubu 5 da 320 da kuma mutuwar mutane dubu 2 da 471 a fadin Najeriya

0 131

Karamar Ministar Sufuri ta Kasa Misis Gbemisola Saraki a yau ta ce tattalin arzikin da ake asarar a hadarurrukan titunan Kasar nan ya kai kusan Naira biliyan 450 cikin kowacce shekara.

Ministar ta bayyana hakan ne a taron bana na Manyan Dillalan Mai na Najeriya wanda taron bitar Kungiyar Direbobi ta NARTO ta shirya a Legas.

Ministar ta ce alkaluman hukumar kiyaye hadurra ta kasa sun nuna cewa an samu hadurran tituna dubu 5 da 320 da kuma mutuwar mutane dubu 2 da 471 a fadin kasarnan a farkon rabin shekarar da muke ciki.

A cewarta, kusan kashi 52 cikin 100 na wadannan hadarurrukan na faruwa ne sanadiyyar gudun wuce sa’a yayin da wasu abubuwan suka hada da munanan hanyoyin da direbobin da ba su cancanta ba da manyan motocin dakon kaya da kuma shaye-shayen miyagun kwayoyi.

Gbemisola Saraki ta ce gwamnatin tarayya a nata bangaren tana yin iya bakin kokarinta wajen gyara hanyoyin kasarnan wanda gwamnatocin baya suka yi sakaci na tsawon shekaru.

Ta ce gwamnati ta fahimci cewa akwai alaka kai tsaye tsakanin sufuri da tsadar kayan abinci a kasarnan, kuma tana kokarin shawo kan lamarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: