An sanar da ranar da za a gudanar da zaben Kananan Hukumomi a jihar Nasarawa

0 144

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Jihar Nasarawa, ta sanar da ranar da za ta gudanar da zaben Kananan Hukumomi a jihar.

Da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa, Shugaban Hukumar, Barista Ayuba Wandai, ya ce za a gudanar da zaben a ranar 2 ga watan Nuwamba, 2024.

Ya ce dokar zaben kananan hukumomi ta jihar da aka yi wa gyara a 2018 ta ba su damar su yi shekara uku ne a kujerar.

Ya ce sun tattauna da shugabannin jami’yyu da ke jihar kuma sun gamsu da tsare-tsarensu.

Haka kuma kowace jam’iyya da ta shiga zaben za ta mika sunayen ‘yan takararta a ranar 29 ga watan Oktoba.

Sannan a gudanar da zaben a ranar 2 ga watan Nuwamba.

Haka zalika za a sauke sunan duk dan takarar da aka same shi a matsayin ma’aikacin Gwamnatin Tarayya ko ta jiha ko ta karamar hukumar da ya tsaya takarar ba tare da ya ajiye aikin ba.

Ya ce masu kada kuri’a za su kasance daga shekara 18 zuwa sama.

Kuma an tanadi matakan tsaro domin gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.

Leave a Reply

%d bloggers like this: