An shawo kan rikicin manoma da Fulani makiyaya a kananan hukumomin Guri da Kirikasamma na jihar Jigawa

0 116

Yanzu haka an shawo kan rikicin manoma da Fulani makiyaya a kananan hukumomin Guri da Kirikasamma na jihar Jigawa.

Shugabannin kananan hukumomin Guri da Kiri Kasamma, sune suka sanar da haka a wata tattaunawa da Jami’in yada labarai na yankin, Sunusi A Doro.

Da yake jawabi shugaban karamar hukumar Guri Alhaji Musa Shu’aibu Muhammad ya ce majalisar karamar hukumar ta gyara motocin ‘yan sanda guda 3, inda ya ce a bana ba a samu asarar rayuka ba sakamakon rikicin tsakanin bangarorin biyu a yankin.

Shugaban ya ce majalisar za ta ware wuraren kiwo domin amfanin makiyayan.

A nasa bangaren shugaban karamar hukumar Kirikasamma Alhaji Isah Adamu Matara ya ce an shawo kan rikicin ne bayan tuntubar juna da kuma ganawa da shugabannin kungiyar manoma da kungiyar makiyaya ta Miyatti Allah da kuma kwamitin tsaro na yankin.

Ya bukaci manoman yankin da Fulani makiyaya da su zauna lafiya da juna domin cigaban karamar hukumar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: