Kotu ta dakatar da gwamnatin tarayya daga cirar dala milliyan 418 daga asusun bankunan Jihohi 36 na kasar nan

0 63

Wata Babbar Kotu a Abuja ta dakatar da gwamnatin tarayya daga cirar Dala milliyan 418 daga Asusun bankunan Jihohi 36 na kasar nan.

Alkalun Kotun Mai Sharia Inyang Ekwo, shine ya bayyana hakan a lokacin da yake yanke hukunci, inda ya bukaci gwamnatin tarayya ta dakatar da kudurinta na cire kudaden, har zuwa lokacin da za’a gama sauraron karar da Jihohi 36 suka shigar gabanta.

A makon da ya gabata ne Gwamnan Jihar Ekiti, kuma Shugaban Kungiyar Gwamnoni Dr Kayode Fayemi, ya bayyana cewa Jihohi baza su lamunci kudurin gwamnatin tarayya na cire wani kason kudade daga Asusun su ba.

Lauyan Jihohi 36 Masu Gabatar da Kara Barista Jibrin Okutepa, ya fadawa Alkalin Kotun cewa Jihohi 36 zasu shiga cikin matsalolin masu tarin yawa, matukar gwamnatin tarayya ta cire Dala miliyan 418 daga Asusun Jihohin.

Barista Jibrin ya ce gwamnatin tarayya ta kuduri aniyar cire Dala miliyan 418 duk wata daga Asusun Jihohi, a matsayin kudin Paris Club.

Leave a Reply

%d bloggers like this: