Mataimakin Shugaban Kasa ya musanta zargin da ake yi na cewa ginin da ya rushe a Legas mallakin sa ne

0 75

Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya musanta zargin da ake yi na cewa ginin da ya rushe a Legas mallakin sa ne.

Wata Kafar Yada Labarai ta shafikan sada zumunta ta rawaito cewa Mataimakin shugaban Kasa Mista Osinbajo, ya sayi filin da ginin benen ya ruso daga hannun Mista Michael Ade ojo, shugaban Kamfanin Elizade Motors.

Amma da yake mayar da jawabi, cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan kafafen yaɗa labarai Mista Laolu Akande, ya fitar, Osinbajo ya ce masu son ta da zaune tsaye ne ke yaɗa wannan jita-jita.

Sanarwar ta kuma ce mataimakin shugaban ba shi da alaƙa da filin ko ginin kamar yadda wasu ke cewa ya sayi filin ne daga hannun wani mutum mai suna Cif Michael Ade. Ojo, Shugaban kamfanin motoci na of Elizade Motors.

Sanarwar ta ce masu yaɗa jita-jitar ba su yi la’akari da halin baƙin cikin da mutanne da suka rasa ƴan uwan a rushewar ginin ke ciki ba, da kuma ƙoƙarin ceto mutane da ma’aikatan agaji ke yi.

Kazalika, Osinbajo ya ce tuni ya tura Lauyoyinsa domin daukar matakan shari’a kan kafar yada labarai da ta kirkiri labarin.

Farfesa Osinbajo ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da waɗanda suka jikkata a lamarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: