‘Yan bindigar da suka sace wasu malamai da ‘ya’yansu daga Jami’ar Abuja sun sake su

0 43

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na cewa ‘yan bindigar da suka sace wasu malamai da ‘ya’yansu daga Jami’ar Abuja sun sake su.

Kimanin Kwanaki 3 kenan yan bindiga suka sace Malaman a rukunin gidajen Ma’aikatan Jami’ar a Gwagwalada.

Kakakin Rundunar Yan Sandan birnin Tarayya Abuja Josephine Adeh, shine ya tabbatar da hakan kubutar da mutanen cikin wata sanarwa, inda ya ce hadin gwiwar Jami’an tsaro ne suka kubutar da malaman.

Cikin Mutanen da akayi Garkuwa dasu sun hada da Farfesoshi 2 da Babban Malami 1 da kuma mutane 3 yan gida daya.

Shugaban Kungiyar Malaman Jami’oi ta Kasa ASUU, reshen Jami’ar Abuja Dr Kasim Umar, ya tabbatar da kubutar da mutanan, inda ya ce ba’a biya kudin fansa ba.

Gidan Talabijin na Channels Tv, ya rawaito cewa a ranar Talata ne ‘yan bindigar suka kutsa cikin rukunin gidajen Ma’aikatan Jami’ar da ke Gwagwalada da misalin karfe daya na dare inda suka sace malamai guda uku da ‘ya’yansu biyu da kuma wani ma’aikacin Jami’ar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: