An tsamo mutum 19 da kwale-kwale ya kife da su a Jihar Sokoto

0 154

Mahukunta a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin kasarnan sun ce ana fargabar mutum 16 sun rasa ransu bayan wani kwale-kwale makare da mutane ya kife.

Kwale-kwalen na ɗauke da manoma ne inda zai kai su gonakinsu na shinkafa a jiya Lahadi.

Hukumar agajin gaggawa ta kasa NEMA, ta ce akwai mutum 19 da suka tsira da ransu.

An gano gawa guda, sannan kuma akwai mata da yara daga cikin waɗanda suka ɓace.

Lamarin ya faru ne a ƙauyen Dundaye.

Masu ninƙaya da kuma masu kamun kifi na cikin waɗanda suka shiga aikin ceton.

Jami’ai sun ce jirgin ya ɗauko ninkin mutanen da ya kamata ya ɗauka ne.

A makon daya wuce ma wasu manoma 15 sun nitse bayan jirgin ruwan da ya ɗauko su ya kife a jihar Jigawa da ke arewacin kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: