A jiya ne wata babbar kotun jihar Jigawa dake zamanta a nan Hadejia ta yankewa Saidu Zakar hukuncin daurin rai da rai bisa samunsa da laifin yiwa wata yarinya ‘yar shekara 11 fyade a karamar hukumar Hadejia.

An kama wanda ake zargin tare da gurfanar da shi a gaban kotu a shekarar 2019 bisa zarginsa da shigar da yarinyar cikin dakinsa tare da yi mata fyade.

Da yake tabbatar da laifin a gaban kotun, lauyan mai gabatar da kara ya gabatar da shaidu biyar tare da gabatar da hujjoji guda uku.

Alkalin kotun, Mai shari’a Ado Yusuf, ya ce laifin ya sabawa sashe na 284 karamin sashe na 2 na dokokin Penal Code na Jihar Jigawa na shekarar 2012 da aka yi wa gyara.

Ya ce lauyan mai gabatar da kara ya tabbatar da aikata laifin ba tare da wata shakka ba.

Don haka ya yankewa wanda ake tuhuma hukuncin daurin rai da rai.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: