An zakulo Gawar mutum bakwai da ambaliyar ruwa ta binne a jihar Neja

0 217

Rahotonni na cewa masu aikin ceto sun zaƙulo gawar mutane bakwai da ambaliyar ruwa ta binne a ƙarƙashin ɓaraguzai a jihar Neja, kamar yadda hukumar agaji ta jihar Nsema ta bayyana.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito shugaban hukumar Abdullahi Baba Arah na cewa hakan ya sa adadin waɗanda aka tabbatar da mutuwarsu ya zama 160 a ranar Talata.

Sai dai alƙaluman sun sha bamban da waɗanda gwamnati ƙaramar hukumar ta bayar na mutane 200.

Abdullahi ya ce mutanen gari ne suka taimaka wajen aikin ceton, inda aka zaƙulo gawa huɗu ranar Litinin, da kuma uku ranar Talata.

A jiya Talata kwamashinan agaji na jihar, Ahmad Sulaiman, ya ce sama da mutane 200 ne suka mutu, sannan ana neman wasu da dama.

Wani jami’in ƙaramar hukumar Mokwa ya faɗa wa BBC cewa ana neman sama da mutane 400 da suka ɓace.

Leave a Reply