Ana Zargin Amarya ’Yar Shekaru 18 da Jikkata Mijinta A Yobe

0 170

’Yan sanda a Jihar Yobe na bincike kan wani lamari da ake zargin wata matar aure ’yar shekaru 18 ta jikkata mijinta a garin Potiskum.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, Dungus Abdulkarim, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe ɗaya na dare a ranar 6 ga Fabrairu, 2026.

A cewarsa, an kai rahoton lamarin zuwa ofishin ’yan sanda na Potiskum da misalin ƙarfe uku na rana a wannan rana, bayan wanda abin ya shafa ya samu rauni mai tsanani.

 Rundunar ta ce wadda ake zargin ta yi amfani da wani abu mai kaifi wajen jikkata mijinta, sannan ta tsere daga wurin kafin isowar jami’an tsaro.

Bayan samun rahoton, ’yan sanda sun garzaya wurin tare da kai wanda abin ya shafa Asibitin Kwararru na Jihar Yobe da ke Potiskum domin samun agajin gaggawa.

Daga bisani, an tura shi zuwa Babban Asibitin Tarayya (FMC) da ke Azare, inda rahotanni ke cewa yana ci gaba da karɓar magani.

Rundunar ’yan sandan ta ce ana cigaba da bincike domin kama wadda ake zargin, yayin da Kwamishinan ’yan sandan jihar, Emmanuel Ado, ya yi Allah-wadai da lamarin, yana mai jaddada cewa yakamata a gina aure akan mutunta juna, haƙuri da fahimta, ba tashin hankali ba.

Leave a Reply