Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Jihar Kano, Abdullahi Abbas, ya ce jam’iyyar a shirye take ta karɓi Gwamna Abba Yusuf idan ya fice daga jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ya koma APC.
Abbas ya ce APC ba za ta ƙi karɓar duk wani ɗan siyasa da ya shigo cikinta ba, yana mai jaddada cewa siyasa wasa ne na yawan mabiya.
“Mun yi maraba da shi a jam’iyyarmu, domin a siyasance babu wani ɗan siyasa mai hankali da zai ƙi ƙarin ƙarfi. Kamar yadda kuka sani, siyasa wasa ce ta adadi,” in ji shi.
“Saboda haka, shigowarsa jam’iyyarmu na nufin ƙara mana yawan mambobi, wanda hakan zai ƙara mana damar samun nasara a zaɓe.”
Abbas ya ƙara da cewa matsayin jam’iyyar ya kasance a bayyane tun da dadewa.
“Mun sha bayyana a lokuta da dama cewa za mu karɓi duk wanda ya ga alherin jam’iyyarmu kuma yake son shigowa cikinta,” in ji shi a wata hira da jaridar Daily Trust.
Game da damuwar batun tikitin kai tsaye (automatic ticket), Abbas ya ce wannan batu bai kai ga lokacin tattaunawa ba.
“Wannan ba batun yanzu ba ne. Batu ne da za a tattauna bayan an kammala dukkan matakai, kuma duk wanda zai shigo jam’iyyar ya kammala tsarin sauya sheƙarsa,” in ji shi.
Ya kuma nuna cewa Gwamna Yusuf ba shi kaɗai zai sauya sheƙa ba.
“Akwai shugabannin ƙananan hukumomi da aka zaɓa, kansiloli da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa da za su biyo shi zuwa jam’iyyarmu,” in ji Abbas.
A cewarsa, batun tsara dabarun siyasa zai zo daga baya.
“Saboda haka, bayan an kammala komai, za mu zauna mu tsara dabarar da kowa zai amfana da ita,” in ji shi, yana mai ƙara da cewa babban burin jam’iyyar shi ne samun nasara a zaɓen shekarar 2027.
“Mun jira zuwansa, kuma ku yarda da ni za mu tsara hanyar da za ta tabbatar da nasarar jam’iyyar cikin haɗin kai, ba tare da wata rigima tsakanin tsoffin mambobi da sababbi ba,” in ji Abbas.
Yana bayyana ra’ayinsa na kashin kansa, ya ce:
“Na yi imani a siyasar Nijeriya, yana da matuƙar wahala ga gwamna mai ci ya faɗi zaɓen fidda gwani (primaries).”
Abbas ya kuma musanta rahotannin da ke cewa an samu jinkiri wajen sauya sheƙar gwamnan. Ya bayyana su a matsayin jita-jita, yana cewa:
“Gwamnan bai fito fili ya ce zai shigo APC a wata rana takamaimai ba.”
Ya bayyana cewa sauya sheƙar gwamna mai ci na buƙatar bin tsari mai tsauri.
“Sauya sheƙar gwamna ba abu ba ne da za a tashi wata rana a ce na sauya jam’iyya,” in ji Abbas.
“Akwai matakai da dole a bi, kuma har sai an kammala waɗannan matakai gaba ɗaya, sauya sheƙar tana nan a matsayin shiri da bai kai ga aiwatarwa ba.”