Shugabar Karamar Hukumar Kano, Sa’adatu Soja, Ta Yi Murabus

0 214

Shugabar Karamar Hukumar Tudun Wada, Hajiya Sa’adatu Salisu Soja Mai Jama’a, ta yi murabus daga jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP).

Ta sanar da murabus ɗinta ne ta cikin wata wasiƙa da ta rubuta ranar Jumma’a, 23 ga Janairu, 2026, wadda ta miƙa wa shugabancin jam’iyyar a Karamar Hukumar Tudun Wada.

A cikin wasiƙar, wadda aka bai wa ‘yan jarida, Sa’adatu ta ce ta yanke wannan shawara ne domin ta bi sahun jagorancin siyasar Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf.

“Na yanke shawarar yin murabus ne domin in bi tafarkin shugabana, Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf, Gwamnan Jihar Kano,” in ji ta.

Ta bayyana cewa ta ɗauki wannan mataki ne bayan yin nazari sosai, domin ta samu damar tallafa wa shirye-shiryen cigaban Jihar Kano da al’ummarta ta hanyar aiwatar da muhimman ayyuka da tsare-tsare masu amfani.

“Dangane da hakan, a nan take nake sanar da yin murabus ɗina daga jam’iyyar,” in ji wasiƙar.

Sa’adatu ta kuma nuna godiyarta ga shugabannin jam’iyyar NNPP da mambobinta bisa goyon baya da suka ba ta a lokacin da take cikin jam’iyyar.

Leave a Reply