Jam’iyar Adawa ta APC a Jihar Bauchi, ta bayyana cewa tayi watsi da Kayan Masarufin da Gwamnan Jihar Bala Muhammad ya bata domin rage radadi cikin watan Ramadana.

Manema labarai sun rawaito cewa cikin kayayyakin da aka kaiwa Jam’iyar a Sakatariyarta sun hada da Shinkafa da Masara da Suga da Taliyar Spaghetti da kuma Dawa.

Jam’iyar ta ce hakan ya sabawa Kundin Jam’iya da kuma Siyasa, musamman daga hannun Gwamnan da yake jagorantar Jihar a karkashin tutar Jam’iyar PDP.

Sakataren Yada Labarai na Jam’iyar APC ta Jihar Bauchi Alhaji Adamu Aliyu Jallah, shine ya tabbatar da hakan ga manema labarai, inda ya ce Jam’iyar ta ki karbar kayan ne saboda bata san manufar raba kayan ba.

Sai dai Shugaban Jam’iyar PDP na Jihar Alhaji Hamza Koshe Akuyam, ya ce bashi da masaniya kan an karbi kayan ko kuma an dawo dashi.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: