Cibiyar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa wato NCDC, ta bayyana cewa an samu sabbin mutane 70 da suka harbu da cutar Corona a Najeriya.

A cewar NCDC, kawo yanzu kimanin mutane dubu 164,303 ne suka harbu da cutar tun bayan bayyanarta a kasar nan.

Haka kuma an sallami mutane dubu 154,384 biyo bayan warkewar su daga cutar, yayinda kuma a gefe guda ta hallaka mutane dubu 2,061.

Cibiyar ta NCDC ta bayyana hakan ne a shafinta na Twitter a Jiya Litinin.

A cewarta, an samu bullar cutar ne a Jihohin 5 da suke Najeriya ciki harda Lagos 27, Kaduna 16, Ondo 16, Yobe 6 and Bauchi 5.

Kazalika, NCDC, ta ce kimanin mutane Miliyan 1 da dubu 870,915 ne aka musu gwajin cutar ta Corona a jihohi 36 ciki harda babban birnin tarayya Abuja.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: