Asirin Ƴan Barka Da Su Ka Sace Jariri A Zariya Ya Tonu

0 177

Wani abu mai kama da almara ya faru akan yadda wasu ’yan barka su ka sacewa wata mata jariri daga zuwa barka a wata unguwa da a ke kira Layin Malam Mai-Bulala da ke garin Samaru a karamar Hukumar Sabon Garin Zariya a jihar Kaduna.

Malama Nafisa ita ce mai jegon da ’yan barkar su ka sacewa jaririn a wata rana gab da sallar Magariba a gidan da take zaune gidan Kyauta Mai-Dissa.

Nafisa ta ce, “wasu matane su biyu kowacce ta saka nikabi a fuskarsu su ka yi sallama da nufin sun zo yi min barkar haihuwa, Bayan sun gaishe ni, sai su ka ce min ina mai gidana? Sai na ce masu ba ya nan, sai su ka ce ai su matan abokinsa ne, sun zo ganin jariri ne tare da mijinsu, wanda ya na waje ya na jiran su.”

Hakan ya sa Nafisa ta amince da ’yan barka har ta dauki jariri ta ba su, su gani bisa al’adar Hausawa da su ka saba.

Amma me zai faru? Mai jego na mika wa wadannan ’yan barka jariri, sai su kuma su ka ce ma ta, “to bari mu kai wa mijin namu jaririn ya ganshi a kofar gida.” Sai mai jego ta ce ma su, “to babu komai.”Bayan ’yan barka sun fito da jariri da kusan minti 30 ne sai mai jego ta ji shiru.

Sai ta fito ta leka kofar gida, ba ta ga kowa ba. Nan take sai ta koma cikin gida ta sanar da jama’ar da ke cikin gida halin da a ke ciki, domin daukar mataki.Bayan sanarwa da sauran jama’ar da ke gida halin da a ke ciki, sai a ka sanar da uban jariri, wanda da ma ya na masallaci ya na sallah.

Nan take ya fito a gigice aka bazama cikin unguwa a na cigiyar wasu mata sanye da nikabi sun sace jaririn gidan Kyauta Mai-Dissa daga zuwa barka.

An kwashe kwana biyu cur ana rokon Allah a masallatai tare da cigiya kan lamarin. A rana ta uku ne sai a ka ji labarin wata mata ta je wata unguwa da a ke kira unguwar Gaiba kusa da gidan mai unguwar da ake kira Malam Hamisu ta jefar da wani jariri.

Hakan ya sa jama’ar da su ka san da maganar su ka dunguma zuwa wancan unguwa tare da mai jegon da a ka sacewa jaririn.

Cikin ikon Allah sai a ka dace yaron da a ka sacen ne aka jefar a wannan unguwar. Nan take mai jego ta dauki jariri ta ba shi nono ya karba ya yi shiru.

Da ma ya na ta tsala kuka. Nan take su ka dawo gida da jariri. Bincike ya nuna cewa, tuni ’yan unguwar da lamarin ya faru suka dauki matakin hana duk wata mata zuwa barkar haihuwar cikin dare. Malama Nafisa ta yi matukar farin cikin ganin jaririnta da a ka sace kuma ta yi godiya da dukkan wadanda su ka taya su addu’a kuma ta yi kira ga dukkan sauran mata ’yan uwanta da su kiyaye da ’yan barka a duk lokacin haihuwa.

Kuma bincike ya nuna cewa a halin yanzu jaririn na samun kulawa, babu wani rauni tare da shi illa ciwon ciki da ya ke fama da shi sakamakon irin madarar da barayin su ka rika ba shi ba ta jarirai ba ce. Uban yaron Malam Yarima ya yi godiya ga dukkan abokan arzuki da su ka taimaka da addu’a. ya ce, Allah ya saka da alkairi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: