Kungiyar kwallon kafan mata ta Super Falcons ta lallasa kungiyar kwallon kafan mata ta Korea Republic daci 2 da nema a wasa na biyu na gasar cin kofin duniya da ake gudanarwa a kasar France.
A yanzu dai Nigeria nada maki 3 daga wasanni 2 data buga inda tayi rashin nasara a wasan farko a hannun kasar Norway daci 3 da nema.
A nan gaba Nigeria zata kara da masu masaukin baki wato France a wasa na 3 na gasar cin kofin duniya ta mata da France take karbar bakunci