ASUU ta zargi gwamnatin tarayya da rashin aiwatar da yarjejeniyar da ta kawo karshen yajin aikin a bara

0 49

Kimanin watanni 9 bayan dakatar da yajin aikin da ya gabata, Kungiyar Malaman Jami’o’i ASUU ta zargi gwamnatin tarayya da rashin aiwatar da yarjejeniyar aiki ta watan Disambar bara wacce ta kawo karshen yajin aikin.

Da yake jawabi ga taron manema labarai a yau, jagoran kungiyar na shiyyar Kano, Kwamared Abdulkadir Muhammad, ya ce kasancewar yajin aikin ba shine kawai zabin da kungiyar ke da shi ba, amma a ko da yaushe shine mafita ta karshe saboda ga dukkan alamu yajin aikin ne kadai yaren da gwamnati ke fahimta.

Ya ce kungiyar ta ASUU za ta yi amfani da duk wata hanya mai ma’ana da dacewa bisa tsarin doka, gami da ci gaba da tattaunawa da jama’a da gwamnati, domin cimma burin ta.

Abdulkadir Muhammad ya ce shiyyar, wacce ta kunshi jami’o’i bakwai, a zaman ta na yau ta sake duba matakin aiwatar da Yarjejeniyar Aiki da Gwamnatin Tarayya ta sanyawa hannu a watan Disambar bara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: