Majalisar Karamar Hukumar Hadejia ta yabawa masu hawa babura da ‘yan achaba bisa bin doka

0 72

Majalisar Karamar Hukumar Hadejia ta yabawa masu hawa babura da ‘yan achaba bisa hadin kan da suke bayarwa ga sabuwar dokar da aka sanya a jiharnan, ta takaita zirga-zirgar babura da dare.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa daga jami’in yada labarai na karamar hukumar, Muhammad Garba Talaki, wacce ya rabawa manema labarai.

Sanarwar ta bayyana cewa gwamnatin jihar Jigawa ta cire babura masu kafa 3 da aka fi sani da Keke Napep, daga cikin wadanda dokar takaita zirga-zirgar ta shafa, wacce take aiki daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe.

Sanarwar tace majalisar karamar hukumar tana umartar masu hawa babura da ‘yan achaba da su cigaba da kiyaye dokar har zuwa lokacin da za a janye ta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: