Jam’iyar APC ta karyata zaben kananan hukumomin Jihar Jigawa

0 81

Shugaban Kwamatin Gudanar da Zabukan Shugabannin Jam’iyar APC na Kananan hukumomin Jihar Jigawa Alhaji Lawan Yunusu ta karyata zargin da ke cewa an gudanar da zabukan daban-daban a jihar nan.

Shugaban ya nanata cewa an gudanar da tarukan zabukan cikin kwanciyar hankali da lumana, inda ya kara da cewa hakan bazai shafi makomar Jam’iyar ba a nan gaba.

Alhaji Yunusa Lawan, ya ce duk da cewa akwai rahotannin da suke cewa an gudanar da tarukan na daban domin nuna adawa da jagorancin Jam’iyar a nan jihar Jigawa, amma Jam’iyar tayi nasarar yin sasanto cikin lumana kamar yadda hakan yake cikin dokokin Jam’iyar.

Haka kuma ya ce kawo yanzu basu samu rahoton korafi daga wuraren mutane ba dangane da zaben shugabannin.

Kazalika, ya ce Jam’iyar zata dauki matakai domin kawar da bambamce-bambamce dake tsakanin mambobin Jam’iyar domin samun hadin kai.

Shima a jawabinsa, Dan Majalisar Jiha Mai Wakiltar Mazabar Hadejia Hon Abubakar Sadiq Jallo, wanda kuma Mamba ne a kwamatin ya ce korafin jajan Jam’iya bayan kammala zabukan Jagororin Jam’iyar ba sabon abu bane.

Leave a Reply

%d bloggers like this: