Goodluck Ebele Jonathan ya ce zaman lafiya shine gadar data hada talauci da Nasara

0 127

Tsohon Shugaban Kasa Dr Goodluck Ebele Jonathan, ya ce zaman lafiya shine gadar data hada talauci da Nasara.

Dr Jonathan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wurin gabatar da wata Mukala mai taken Hanyoyin Magance Ta’addanci da Kisa a Najeriya wanda gidauniyarsa ta Goodluck Jonathan Foundation ta shirya a Abuja.

Tsohon Shugaban Kasar ya ce ya gano cewa zai yi wahala a samu zaman lafiyar kasar nan, matukar ba’a magance matsalolin tsaro ba, biyo bayan yadda ya mulki kasar nan tsawon shekaru 5 kuma ya iya gano hakan.

A cewarsa, samar da zaman lafiya zai yi wahala a kasar nan, matukar ba’a magance matsalar rashin adalci ba, da kuma sauran bukatun mutane.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN, ya rawaito wurin da tsohon shugaban kasar ya ce cewa talauci na daga cikin abubuwan da suke jefa mutane aikata laifuka tare da bijirewa Doka da Oda.

Tun farko a Jawabinta, Daraktar Gidauniyar Goodluck Jonathan, Foundation Misis Ann Iyonu, ta ce samar da zaman lafiya shine abinda zai ciyar da Nahiyar Afrika gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: