NCDC ta ce karin mutum 466 ne suka kamu da cutar korona a Najeriya

0 119

Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa ta Kasa, NCDC, ta ce karin mutum 466 ne suka kamu da cutar korona a faɗin ƙasar a ranar Juma’a.

NCDC ta ce an samu mutanan ne daga jihohi 12 da suke Najeriya ciki harda birnin tarayya Abuja.

Hukumar ta ce akasarin waɗanda suka kamu da cutar a jihar Legas suke inda aka samu ƙarin mutum 134 da suka kamu da cutar a jihar yayin da jihar Ribas aka samu mutum 82 da suka kamu da cutar sai kuma Edo mutum 69.

Sauran Jihohin sune Gombe (39), FCT (32), Kaduna (21), Plateau (20), Benue (19), Kwara (17), Delta (16), Akwa Ibom (10), Bayelsa (5) and Kano (2).

Cibiyar ta NCDC ta ce a jiya Juma’a an sallami mutane 183 da suka warke daga cutar, a yayin da kuma ta hallaka karin mutane 3 a jiyan.

Kawo yanzu kimanin mutane dubu 2,588 ne cutar Corona ta hallaka a kasar nan baki daya.

Daga watan Fabreru na shekarar 2020 zuwa yanzu kimanin mutane dubu 198,239 ne suka harbu da cutar Corona, kuma cikinsu anyi nasarar Sallamar mutane dubu 185,780 bayan sun warke gaba daya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: