NAFDAC ta gargadi ‘yan Najeriya game da amfani da man girki mai cutar da lafiyar jiki

0 71

Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta gargadi ‘yan Najeriya game da amfani da man girki mai dauke da magungunan da ke cutar da lafiyar jiki.

Darakta Janar ta hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta yi wannan gargadin lokacin da ta kaddamar da gangamin wayar da kai a shiyyar Arewa ta Tsakiya da aka gudanar jiya a birnin Ilorin.

A yayin da take jawabi bayan gangamin wayar da kan a manyan kasuwanni da hanyoyi a cikin birnin Ilorin, shugabar ta NAFDAC ta ce makasudin gangamin shine kare mutane daga illolin abinci mara kyau da kayayyakin asibiti na jabu da kayan kwalliya masu cutarwa da gurbataccen ruwan sha da sauran su.

A cewarta, wasu ‘yan kasuwa maza da mata a yunkurin samun riba, suna gauraya man ja da wani sinadari mai suna Azo Dye wanda ke iya haifar da cutar daji ta kansa.

Ta ce an shirya gangamin da niyyar magance matsalolin kiwon lafiyar al’umma kamar shan miyagun kwayoyi musamman tsakanin matasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: