Wata kotu da ke jihar Kano ta tsare wani yaro a gidan gyaran da’a bisa zargin fashi da makami

0 77

A yau ne wata Babbar Kotun Majistare da ke Jihar Kano ta tsare wani yaro dan shekara 17 a gidan gyaran da’a bisa zargin fashi da makami.

Yaron wanda yake zaune a karamar hukumar Kura ta jihar Kano, yana fuskantar tuhuma bisa laifuka biyu na hadin baki da fashi.

Mai gabatar da kara, Asma’u Ado, ta shaidawa kotun cewa wanda ake kara ya aikata laifin ne a ranar 23 ga watan Yuli a Garin Kura da ke jihar Kano.

Asma’u Ado tace wanda ake kara ya hada baki da wani yaro dan shekara 17, domin yi wa wata mata mai suna Aisha Muhammad fashin wayarta.

Mai gabatar da kara tayi zargin cewa su biyun sun caka wa wacce suka yiwa fashin, wuka a ciki, sannan suka kwace wayarta kirar Vivo, wacce ba a bayyana darajar kudinta ba.

Ta shaida wa kotun cewa ana shirin gurfanar da su tare daya yaron sai ya mutu yayin da yake fama da cutar kwalara a Asibitin Cututtuka masu yaduwa na Kano a ranar 24 ga watan Augusta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: