Atiku Abubakar ya ce ya kamata a riƙa matsawa iyaye da su shigar da ƴaƴansu da ɗakunan karatu a makarantu kamar yadda ake yiwa allurar Corona

0 166

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce kamar yadda ake jan hankalan ‘yan kasar da su yi allurar rigakafin cututtuka kamar cutar shan inna da cutar korona, ya kamata a rika matsawa domin tabbatar da cewa iyaye sun shigar da ‘ya’yansu da dakunan karatu a makarantu.

Atiku, ya ce wani lokaci a baya hukumomi sun taba daure mahaifinsa a gidan yari saboda ya ki sa shi makaranta tun yana karami, ya ba da shawarar cewa a ja hankalin iyaye, har ma a tilasta musu su tura ‘ya’yansu makaranta domin akalla su samu ilimin zamani.

Ya ce wannan ita ce hanya daya tilo da za a rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a kasar,

Kawo yanzu dai alkaluman yaran da basa zuwa makarantar a kasar nan ya ta samma  sama da miliyan 13.

Dan siyasar ya ba da wannan nasihar ne a cikin lakcar da ya gabatar a karshen mako a wajen wani taro a jami’ar Achievers da ke Owo, jihar Ondo, inda ya yi jawabi mai taken; Bambance-bambancen karatu, Ilimi da cin gashin kai: Ci gaban Najeriya a cikin shekaru masu zuwa

Leave a Reply

%d bloggers like this: