Atiku ya kai wa Buhari ziyara a gidansa dake Daura

0 117

Dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar PDP a zaben daya gabata Atiku Abubakar ya kai ziyara ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buharia gidansa dake Daura a jihar Katsina.

Atiku wanda ya samu rakiyar tsohon gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal tare da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP, sun shiga wata tattaunawar sirri a gidan tsohon shugaban kasar.

Ziyarar Atiku ga Buhari na zuwa ne kwanaki 3 bayan ya kai makamanciyar ta ga tsohon shugaban kasa na mulkin soja Ibrahim Babangida da kuma Tsoho shugaban kasa Abdussalam Abubakar a gidajen su dake jihar Niger.

Mazauna garin Daura sun gaywa manema labarai cewa ziyarar ta Atiku bata rasa nasaba da zaben 2027 dake tafe.

Atiku ya kasance tsohon mataimakin shugaban kasa, wanda yayi aiki tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007.

Leave a Reply

%d bloggers like this: