Tsohon Mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar kuma dan takarar neman kujerar shugabancin kasar da ya sha kaye, ya soki matakin gwamnatin kasar na shirin kashe Dala biliyan guda da rabi wajen gyaran matatar man Fatakwal, inda ya bukaci sayar da shi baki daya.

Atiku Abubakar ya bukaci bayani daga gwamnati kan yadda aka yi aka amince da kudin gyaran lura da yadda gwamnati ke cigaba da tafka asara wajen kashe kudaden gyara matatun man da kasar ke da su.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bukaci mikawa ‘yan kasuwa matatun domin ganin an gudanar da su ta hanyar da ya kamata.

Atiku Abubakar wanda ke ganin sayar da matatun man kadai ne zai ceto Najeriyar daga asarar da ta ke tafkawa da kuma farfado da tattalin arzikinta, ko a yakin neman zabensa na 2019 ya bayyana aniyarsa ta mika katafaren kamfanin man kasar NNPC ga ‘yan kasuwa.

Tsohon mataimakin shugaban Najeriyar da ya shafe shekaru 8 a mulki, ya ce asara ce ci gaba da zuba kudi ga matatun man da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ke ci gaba da yi tsawon lokaci ba tare da ganin nasara ba.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: