Babu abin da zai faru don an tsige Fubara – Wike

0 84

Tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya ce babu abin da zai faru idan majalisar dokokin jihar ƙarƙashin jagorancin Amaewhule sun tsige gwamnan jihar, Siminalayi Fubara.

A wata hira da manema labarai da ya gabatar ranar Laraba a Abuja, Mista Wike ya ce ƴanmajalisar ba su yi laifi ba idan suka yanke shawarar tsige Fubara, saboda ya aikata laifukan da suka cancanci a tsige shi, ciki kuwa har da riƙe musu albashi na tsawon watanni.

”Idan har ka aikata laifin da ya kamata a tsigekan, mene ne laifi idan an tsigekan? ba laifi ba ne ,kundin tsarin mulki a tanadi hakan…” a cewar Mista Wike – wanda shi ne minitan Abuja.

“Idan ka yi abin da ya saɓa kundin tsarin mulki, kuma majalisa ta ga dacewar tsigeka, dole a tsigeka, babu abin da zai faru,” a cewarsa.

“Na ji mutane na cewa: ‘Idan aka tsige shi hakan zai kawo hargitsi da rashin zaman lafiya, wannan shirme ne babu abin da zai faru.

”Gwamnan Fubara ya samu matsala da tsohon gwamnan jihar, bayan soma gudanar da mulki, wani abu da ya saƴansiyasar biyu suka ja zare a fagen siyasar jihar, mai arzikin man fetur.

– BBC Hausa

Leave a Reply