Hukumar lafiya ta kasar Sin, ta bayyana a yau Litinin cewa, ya zuwa jiya Lahadi, ba a samu rahoton wanda ya kamu da COVID-19 a cikin babban yankin kasar ba.

Sai dai hukumar ta bayyana yayin rahoton da ta saba bayarwa a kowace rana cewa, a jiyan an samu rahoton sabbin mutane biyar da suka shigo da cutar daga ketare. Haka kuma babu rahoton sabbin masu kamuwa ko wadanda suka mutu sanadiyar cutar.

A kuma jiyan, an sallami mutane 13 daga asibitoci daban-daban, bayan da aka tabbatar sun warke daga cutar.

A cewar hukumar, ya zuwa jiya da dare, an samu rahoton mutane 5,146 da suka shigo da cutar cikin babban yankin kasar daga ketare. Daga cikin wannan adadi, an sallami mutane 4,975 daga asibitoci daban-daban, bayan sun warke daga cutar, an kuma kwantar da mutane 171. Amma kuma babu rahoton wadanda suka mutu daga cikin wadanda suka shigo da cutar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: