Badaru Abubakar ya ce sauya dabarun tsaro ne abun da ya kamata a mayar da hankali ba wai taro kan tsaro ba
Ministan tsaro, Mohammad Badaru Abubakar ya ce sauya dabarun tsaro ne abun da ya kamata a mayar da hankali ba wai taro kan tsaro ba, da majalsair dattawwan ƙasar ta nemi a yi ba.
Haka kuma ya musanta zargin da majalisar wakilan ƙasar ta yi na cewar ƴan bindigar na amfani da makaman da suka fi na jam’an tsaron ƙasar.
A ranar Talata ne dai majalisar dattawa suka buƙaci da a shirya wani taro kan harkokin tsaro, don samar da hanyoyin magance matsalar.
Sai dai a yayin ganawa da manema labarai na ministoci da ya gudana a jiya Laraba ministan tsaron Mohammad Badaru Abubakar ya ce sake dabarun yaƙi da matsalar tsaro ya kamata a yi ba wai taro ba a halin da ake ciki a ƙasar.
Acewar Badaru shirya taron ƙasa kan tsaro, zai bawa mutane damar bayyana ra’ayoyin su dangane da abinda matakan da suke, ta yadda za a sake sabunta tsarin tsaron kasa, sannan sai babban hafsan tsaron ƙasa shi ma ya bayar da umarni bisa dabaru da tsarin da aka bayar.