Hukumar jindadin Alhazai ta jihar jigawa ta gudanar da wani taro da shugabanin shiyya shiyya da kuma jami’an alhazai na kananan Hukumomi Jihar nan 27 a helkwatar hukumar dake Dutse gabannin Fara jigailar maniyatan aikin hajjin bana
Darakta Janar na Hukumar Alhji Ahamed Umar labbo ya ce taron yana da muhimmanci kasancewar aiki ya yi nisa na fara jigilar maniyata zuwa kasa mai tsarki
Alhaji Umar labbo yace hukumar ta kammala duk wani shiri ga maniyata domin fara jigilar su zuwa kasa mai tsarki.
Darakta Janar yace a lokacin taron da suka gudanar da jami’an sun rabawa shugabanin shiyya shiyya da jami’ansu dukkanin kayayyakin maniyata da sauran muhimman abubuwa da suke kamat
Ya kuma ce an kammala yiwa maniyatan biza kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci za a iya kiran maniyatan ta gidajen radio zuwa sansanin alhazai domin dibarsu zuwa kasa mai tsarki
Daga nan sai ya hore shugabanin shiyya shiyya da suyi taka tsantsan da kayayyakin maniyata saboda mahimmacinsa