Shugaban kwamatin tuntuba da tsare-tsare na jam’iyyar APC na kasa kuma gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar ya ce jam’iyyar zata gudanar da babban taronta a watan Yuni mai zuwa.

Da yake ganawa da manema labarai a Sakatariyar jam’iyyar dake Abuja, gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya ce kwamatin ya himmatu wajen gudanar da ayyukansa kafin watan Yuni mai zuwa.

Ya ce kwamatin zai yi aiki tare da babban kwamatin riko na jam’iyyar wajen sauke nauyin da aka dora masa.

Ya kara da cewar kwamatin tuntuba da tsare-tsaren zai sasanta wadanda aka sabawa da kuma janyo wadanda ba yan jam’iyyar ba cikin jam’iyyar, inda ya ce suna da yakinin cewar jam’iyyar APC zata kasance jam’iyya daya tilo a kasar nan.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: