Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada tsohuwar ministar harkokin mata da walwala, Salamatu Suleiman, a matsayin shugabar hukumar kare hakkin bil’adama ta kasa.

Salamatu Suleiman ta rike mukaman ministar harkokin mata da karamar ministar harkokin waje a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar’adua.

Kazalika ta rike mukamin kwamishinar harkokin siyasa, zaman lafiya da tsaro a kungiyar cigaban raya kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) daga shekarar 2012 zuwa 2016.

Shugaban kasa ya kuma nada wasu mambobi 14 na hukumar gudanarwar hukumar kare hakkin bil’adama ta kasa. Hakan yazo ne a wasikar da ya rubutawa majalisar dattawa yana neman amincewarta da tabbatar da wadanda ya nada.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: