Bai dace ba a jefa rayuwar yara cikin hadari ta hanyar barinsu shiga zanga-zanga – Dr Muhd Sani

0 113

Hukumar kula da ilimin almajirai da yara masu gararanba a titi ta nuna rashin jin dadinta kan yadda yara kanana suka shiga zanga-zangar matsin rayuwa da ake yi a kasar.

A wata sanarwa da ta fitar hukumar ta ce duk da cewa zanga-zangar ‘yanci ne da jama’a suke da shi na su bayyana ra’ayinsu to amma ta ce bai dace ba a jefa rayuwar yara cikin hadari ta hanyar barinsu shiga wannan zanga-zanga.

Sakataren zartarwa na hukumar Dr Muhammad Sani ya ce, ganin yadda yara, wadanda ya kamata a ce suna makaranta, da kuma kila ba sa zuwa makarantar suke shiga zanga-zangar musamman a arewacin kasar hakan ya nuna irin gagarumin aikin da ke gabansu. A don haka shugaban ya yi kira ga iyaye da masu kula da ‘ya’ya da yaransu, sannan su rika bayar da fifiko ga lafiya da rayuwarsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: