Ban ci amanar Atiku ba, na fahimci Shugaba Tinubu na da kaifin tunani fiye da masu yi masa adawa – Segun Sowunmi
Ɗan jam’iyyar PDP, Segun Sowunmi, ya bayyana cikakken ‘yancinsa na siyasa bayan ganawa da Shugaba Tinubu da ta haifar da ce-ce-ku-ce daga magoya bayan Atiku Abubakar.
A wata hira da ya yi da Channels TV, Sowunmi ya ce ganawarsa da Tinubu ba na cin amanar Atiku ba ne, amma yana girmama wayewar siyasar da Tinubu ke da ita fiye da abokan hamayya irin su Peter Obi.
Ya ce yana da ikon fadin ra’ayinsa kuma ya san abin da ya ke so, yana mai jaddada cewa a siyasance mutum zai iya gane ƙwarewar wanda ke gaba da shi ba tare da barin jam’iyyarsa ba. Ganawar tasa ta shiga jerin sauyin yanayi da ake gani daga wasu abokan Atiku da suka hada da Daniel Bwala, da hakan ke ƙara hasashen canjin salo gabanin 2027.