Dole ne malami ya mallaki digirin Master’s tare da albashin Naira dubu 400 a wata – Alex Oyia

0 569

Masanin ilimi kuma shugaban kamfanin Educare, Alex Onyia, ya bukaci a yi gyara na gaggawa a tsarin koyarwa a Najeriya, yana mai cewa dole ne malami ya mallaki digirin digirgir (master’s) tare da albashin da bai gaza Naira dubu 400 a wata ba.

Ya bayyana ƙasar Finland a matsayin abin koyi, inda ya ce kyakkyawan albashi da kwangila mai amfani za su jawo ƙwararru su koya wa yara makarantun gaba.

A ra’ayinsa, dole ne a bai wa malamai motoci, rancen gida da horo na ci gaba da ke da nasaba da lasisin koyarwa domin inganta ƙwarewa da ƙarfafa kwazo.

Sai dai wasu sun yi tir da shawarar, suna masu cewa bata dace da yankunan karkara ba, yayin da wasu ke ganin daidaita tsarin a bisa gaskiya da inganci shi ne mafita fiye da takardar karatu kaɗai.

Leave a Reply