Jam’iyyar APC mai mulki ta yi barazanar ladabtar da Sanata Ali Ndume bisa kalaman sa ga Shugaban Kasa
Jam’iyyar APC mai mulki ta yi barazanar ladabtar da Sanata Ali Ndume bayan ya bayyana fargabar cewa shugaba Bola Tinubu na iya fuskantar irin kaddarar da ta samu tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a zaben 2027, saboda tsadar rayuwa da shakku daga cikin jam’iyyar.
Sanata Ndume ya danganta halin da ake ciki da yadda abubuwa suka kasance kafin 2015, lokacin da Jonathan ya sha kaye duk da goyon baya daga manyan kusoshin siyasa.
Sai dai daraktan yaɗa labarai na jam’iyyar APC, Bala Ibrahim, ya ce kodayake Ndume na da ‘yancin fadar ra’ayinsa, jam’iyyar ba za ta lamunci sabawa ƙa’ida da haddasa rudani ba, musamman ganin yadda batun tikitin kai-tsaye ke tayar da kura a matakin ƙananan ‘ya’yan jam’iyya. Duk da haka, APC ta ce tana buɗe kofar gyara da shawarwari matuƙar dai za a yi hakan cikin tsarin ci gaba da haɗin kai.