Gwamnatin jihar Borno ta yi kira ga gwamnatin shugaba Tinubu ta hanzarta daukar mataki kan ɗan kwangilar da ta baiwa aikin yashe dam din Alou da ya haifar da ambaliya a bara.
Ta ce duk da cewar sun yashe wani sashe na dam din amma, har yanzu akwai babbar barazana da za a iya fuskantar mumunar ambaliya.
Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin tsaro na jihar Borno, Farfesa Umar Tar da harkkokin tsaro ya shaida wa BBC cewa an bayar da kwantaragin kuma minista ya je ya ƙaddamar da aikin.
“Har yanzu ba mu ga ƴan kwangila sun zo domin fara aikin ba kuma yanzu ga damuna ta riga ta sauka. Idan ba a yi aikin nan da wuri ba to idan ruwa ya zo ya yi halinsa to lallai za a samu matsala. Ya kamata ace an yashe ruwan saboda irin cunkushewar da ya yi. Idan aka yashe shi to ko ruwa ya zo da yawa ba zai ambaliya ba.” In ji Farfesa Tar.
A damunar bara ne dai madatsar ruwa ta Alo Dam ta cika ta tunbatsa inda ta kuma karye wani abu da ya janyo ambaliyar ruwa da ya haddasa asarar rayuka da ta dukiyoyi a birnin Maiduguri.