Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ɗauki matakai masu wahala amma masu matukar amfani domin ceto Najeriya daga matsalar tattalin arziki da ta addabi ƙasar.
A wani sharhi da ya wallafa, Onanuga ya ce duk da sukar da masu adawa ke yi wa gwamnatin Tinubu, sauye-sauyen tattalin arzikin da aka aiwatar cikin shekaru uku da suka gabata sun fara haifar da sakamako mai kyau a faɗin ƙasar.
Ya ce daga cikin matakan da gwamnatin ta ɗauka akwai cire tallafin man fetur, daidaita farashin canjin kuɗi da kuma sake fasalin tsarin kuɗaɗen gwamnati, waɗanda a cewarsa suka ƙara kuɗaɗen shiga ga jihohi da ƙananan hukumomi.
Onanuga ya bayyana cewa jihohi da dama da a baya ke fama da matsalar biyan albashi da gudanar da ayyukan raya ƙasa yanzu suna aiwatar da manyan ayyukan ci gaba sakamakon ƙarin kuɗaɗen da suke samu daga asusun tarayya.
Ya kuma yi nuni da cewa kasuwar hannayen jari ta samu gagarumar bunƙasa, yayin da masu zuba jari daga ƙasashen waje ke ƙara nuna sha’awa ga tattalin arzikin Najeriya.
Dangane da ayyukan more rayuwa, ya ce gwamnatin Tinubu na gudanar da manyan ayyukan tituna da layukan dogo a sassa daban-daban na ƙasar, ciki har da titin Lagos-Calabar da kuma hanyar Sokoto zuwa Badagry.
Onanuga ya ƙara da cewa gwamnatin na ci gaba da zuba jari a fannoni kamar ilimi, makamashi, noma da tsaro domin samar da ingantacciyar rayuwa ga ‘yan Najeriya.
Sai dai ya amince cewa har yanzu ƙasar na fuskantar ƙalubalen tsaro, musamman hare-haren ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane, amma ya ce gwamnati na ci gaba da bai wa jami’an tsaro kayan aiki da tallafin da suke buƙata domin murƙushe barazanar.
Ya zargi masu adawa da ƙoƙarin rage darajar nasarorin gwamnatin Tinubu, yana mai cewa tarihi zai tuna da shugabancin Tinubu a matsayin wanda ya ɗauki matakan da suka taimaka wajen ceto tattalin arzikin Najeriya daga matsaloli masu tarin yawa.