Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Dijital, Sheikh Professor Isa Ali Pantami, ya tabbatar da cewa ya dade da ficewa daga jam’iyyar APC, inda ya ce tun ranar 19 ga watan Mayun 2026 ya miƙa takardar ficewarsa daga jam’iyyar a hukumance.
A cikin wata sanarwa da Comrade Abba Sani Pantami ya fitar, ya bayyana cewa shugaban APC na gundumar Pantami ya sanya hannu tare da tabbatar da karɓar takardar yadda ya kamata.
Sanarwar ta ce an ɗauki wannan mataki ne bayan dogon nazari da tattaunawa da masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na jihar Gombe da ma wasu wurare.
A cewar sanarwar, Pantami ya bayyana cewa an yanke shawarar ne bayan yin cikakken nazari kan inda zai fi iya yi wa al’ummar jihar Gombe hidima yadda ya kamata.
Professor Pantami ya kuma sake jaddada aniyarsa ta ci gaba da fafutukar ganin ci gaban jihar Gombe da kyautata rayuwar al’umma.
Sanarwar ta ƙara da cewa siyasa ya kamata ta kasance bisa hidima, gaskiya da kuma hangen nesa domin tabbatar da kyakkyawar makoma ga al’umma.