Gawuna Ya Amince Da Takarar Sanata

0 164

Tsohon mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo ya zama ɗan takarar gwamna na jam’iyyar NDC a jihar Kano gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Majiyar siyasa ta tabbatar da cewa, babban mai neman takarar jam’iyyar, Nasiru Yusuf Gawuna, ya amince da tikitin takarar Sanatan Kano ta Tsakiya bayan doguwar tattaunawa da masu ruwa da tsaki da kuma magoya bayansa.

Rahotanni sun nuna cewa Gawuna ya fara nuna rashin amincewa da tayin takarar sanatancin, sai dai daga bisani ya sauya matsayi bayan tuntuba.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da sauye-sauyen siyasa da sasanta rikice-rikice tsakanin manyan ‘yan siyasa a Kano, yayin da jam’iyyu ke ƙara ɗaukar matakai domin shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027.

Leave a Reply