Jam’iyar PDP zata shiga fafatawar zaben Kananan Hukumomin Jihar Jigawa da yan Takarkaru 6 Kacal cikin kananan hukumomi 27 da suke fadin jihar nan.

Shugaban Jam’iyar PDP na Jihar nan Babandi Ibrahim, shine ya bayyana hakan, inda ya ce sauran yan takarkarun baza su Iya siyan Forms din Nagani Inaso ba, na neman Takarar wanda hukumar Zabe ta Jiha ta fitar ba, saboda tsadarsa.

A cewarsa, hukumar Zabe ta sanya Naira dubu 500,000 a matsayin kudin Form Forms din Nagani Inaso ba, na dan takarar karamar hukumar, yayinda kuma ake sayarda Form din Dan takarar Kamsila akan Naira dubu N200,000.

Babandi Ibrahim, ya ce hukumar zaben ta karya dokokin Democradiya, inda ya bayyana cewa hukumar INEC bata sayar da Form din Na gani Ina so ba kamar yadda ake kokarin yi a yanzu.

Manema Labarai sunyi kokarin jin ta bakin Shugaban Hukumar Zabe ta Jihar Jigawa Adamu Ibrahim, sai dai basu samu damar ganinsa ba a ranakun Talata da Laraba da kuma Alhamis.

Sai dai Mataimakin Gwamnan Jiha Malam Umar Namadi, ya fadawa manema Labarai cewa sauran Jam’iyun Adawa suna cikin wadanda zasu shiga zaben, inda ya bada tabbacin cewa za’ayi Adalci a zaben.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: