Yan Bindigar sun kashe mutum 1 da tare da yin garkuwa da mutane 33, biyo bayan harin da suka kai a karamar hukumar Kachia ta Jihar Kaduna.

Yan bindigar sun kai harin ne a shekaran Jiya da daddare a cikin birnin Kachia, tare da raunata mutane da dama.

Hakimin Kachia Malam Idris Suleiman, shine ya tabbatar da hakan a lokacin da Tawagar tsaro karkashin Jagorancin Kwamishinan Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida Mista Samuel Aruwan suka ziyarci yankin.

A cewarsa, yan bindigar sun mamaye garin ne akan Babura da misalin karfe 9 na Dare, inda suka dinga harbe-harbe a sararin Samaniya domin razana mutane.

Hakimin Kachia, ya ce yan bindigar sun sace mutane 5 a wani gidan Biredi, tare da kashe Direban mai gidan Biredi, inda ya kara da cewa sun sake sace Mutane 28 ciki harda wata Mata mai ciki a yankin Mother Cat.

Haka kuma ya ce yan Bindigar sun fasa shagunan mutane tare da wawushe kayayyakin yan Kasuwa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: