Shugaba Buhari ya yi rabon gidaje ga tawagar ’yan kwallo da suka lashe AFCON

0 74

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi rabon gidaje ga tawagar ’yan kwallon Najeriya da suka lashe Gasar Cin Kofin Kasashen Afirka ta AFCON da aka buga a Tunisia a shekarar 1994.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Mallam Garba Shehu shine ya fidda sanarwar hakan a ranar Alhamis, inda ya ce hakan wani mataki ne na cika alkawarin da gwamnatin Tarayya ta yi.

Mallam Shehu ya ce za a bai wa kowanensu wadataccen gida mai dakunan kwana uku a duk jihar da suke so a fadin kasar nan kamar yadda wata sanarwar da Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Raji Fashola ya fitar.

Sanarwar ta ce tuni shida daga cikin ’yan tawagar kwallon kafar ciki har da ma’aikatansu sun mallaki nasu gidajen.

Daga cikin wadanda suka samu wannan tagomashi akwai, Peter Rufai, Alloy Agu, Ike Shorounmu, Uche Okechukwu, Samson Siasia, Efan Ekoku, Sunday Oliseh, Benedict Iroha, Isaac Semitoje, Mutui Adepoju, Emmanuel Amukike, Victor Ikpeba, Austin Eguavoen da marigayi Wilfred Agbonavbare.

Sauran sun hada da marigayi Uche Okafor, marigayi Thompson Oliha, marigayi Stephen Keshi, Christian Chukwu, Dokta Akin Amao, Stephen Edema, Kanal A Asielue da B. Aromasodun.

Leave a Reply

%d bloggers like this: