Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai tafi birnin London na Kasar Burtaniya a yau Juma’a don duba Lafiyarsa, a cewar fadar shugaban Kasa.

Kakakin Shugaban Kasa Femi Adesina shine ya bayyana hakan, inda ya bayyana cewa Shugaba Buhari zai tafi London ta kasar Birtaniya a ranar Juma’a, 25 ga watan Yuni 2021, don komawa ya sake bibiyar lafiyarsa.

Femi Adesina ya ce Shugaba Buhari zai dawo Najeriya ne a mako na biyu cikin watan Yulin da ke tafe.

A watan Maris Buhari ya kai ziyara birnin na London inda ya je duba Lafiyarsa, ya kuma kwashe kusan mako biyu a can kafin ya koma gida.

Wannan ita ce ziyara ta biyu cikin watanni uku da shugaban zai je London don ganin likita.

Kazalika, Femi Adesina ya ce Shugaba Buhari baya bukatar ya mika Mulki ga Mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: