Gwamnatin Jihar Jigawa ta yanke Shawarar Cigaba da gudanar da Rigakafin Allurar Shan Inna ta Polio

0 115

Gwamnatin Jihar Jigawa ta yanke Shawarar Cigaba da gudanar da Rigakafin Allurar Shan Inna ta Polio, duk da cewa an shafe tsawon Shekara 9 ba tare da an samu bullar cutar ba.

Daraktan Hukumar Lafiya a Matakin Farko ta Jiha Dr Sambo Shehu, shine ya bayyana hakan ga manema labarai a Dutse.

A cewarsa, kimanin Yara Miliyan 1 da dubu 700 za’a yiwa Rigakafin Allurar Polio wanda za’a gudanar daga ranar 28 ga watan Yuni zuwa 3 ga watan Yuli na shekarar 2021.

Dr Sambo Shehu, ya ce gwamnatin jiha ta dauki matakin ne domin dakile bullar cutar, tare da bawa Yara Kariya daga cutar.

Haka kuma ya ce za’a gudanar da Rigakafin ne a kananan hukumomi 27 da suke fadin jihar nan.

Daraktan, ya kuma bukaci Malaman Addinai, da masu sarautun gargajiya su tallafawa shirin domin kaiwa ga Nasara.

Kazalika, ya ce hukumar ta dauki Ma’aikatan wucin gadi dubu 13,000 domin gudanar da rigakafin, ciki harda Ma’aikata dubu 3,060 wanda zasu rika shiga gida-gida da Tawagar Kwararru su 546 da kuma Ma’aikatan Lafiya 776.

Leave a Reply

%d bloggers like this: