Hukumar zaben Jigawa ta karya dokokin Dimokuradiyya, Inji shugaban PDP

0 67

Shugaban Jam’iyyar PDP reshen jihar Jigawa, Babandi Ibrahim, ya ce hukumar zaben ta karya dokokin Democradiya, inda ya bayyana cewa hukumar INEC bata sayar da Form din Na gani Ina so ba kamar yadda ake kokarin yi a yanzu.

Manema Labarai sunyi kokarin jin ta bakin Shugaban Hukumar Zabe ta Jihar Jigawa Adamu Ibrahim, sai dai basu samu damar ganinsa ba a ranakun Talata da Laraba da kuma Alhamis.

Sai dai Mataimakin Gwamnan Jiha Malam Umar Namadi, ya fadawa manema Labarai cewa sauran Jam’iyun Adawa suna cikin wadanda zasu shiga zaben, inda ya bada tabbacin cewa za’ayi Adalci a zaben.

Leave a Reply

%d bloggers like this: